A farkon sabuwar shekara, aka nada Qin Gang, a matsayin ministan harkokin wajen kasar, ya kuma fara kai ziyarar aiki a kasashen Afirka. Ziyarar da ministocin wajen kasar Sin ke kaiwa Afirka a farkon kowa ce shekara, wata al’ada ce ta diflomasiyya ta kasar Sin a cikin shekaru 33 a jere, ba wai kawai tana nuna kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ba, har ma tana nuna cikakken goyon bayan da kasar Sin ke bayarwa ga ci gaba da farfado da nahiyar Afirka, wadda ke da kasashe masu tasowa da dama.
A karshen shekarar 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya je Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya, don halartar taron koli na farko na Sin da kasashen Larabawa, da kuma taron kolin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa karo na farko, kana ya yi shawarwari da shugabannin kasashen Larabawa kusan 20, domin tsara hanyar gina al’ummar Sin da na Larabawa mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
A watan Nuwamba na shekarar 2022, birnin Beijing ya tarbi shugaban kasar Latin Amurka da Caribbean na farko da ya kawo ziyara kasar Sin bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, wanda shi ne sakataren farko na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta Cuba, kuma shugaban kasar Miguel Díaz-Canel Bermúdez. A yayin ganawar, shugabannin kasashen biyu sun amince da yin hadin gwiwa tare don gina al’ummar Sin da Cuba mai makomar bai daya, a kokarin sa kaimi ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama, tare da ciyar da dangantakar Sin da Latin Amurka a sabon zamani bisa daidaito,da samun moriyar juna, da kirkire-kirkire, da bude kofa, da kuma amfanar da jama’a gaba daya yadda ya kamata.
A yammacin ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2022, Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Indonesia Joko Widodo a tsibirin Bali, inda suka cimma matsaya mai muhimmanci kan gina al’ummar Sin da Indonesia mai kyakkyawar makomar bai daya, sun kuma amince da yin amfani da bikin cika shekaru 10 da kafuwar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Indonesia a shekarar 2023, a matsayin wata dama ta samar da wani sabon salon hadin kai mai inganci.
Bugu da kari, bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa su ne muhimman manufofin diplomasiyya da kasar Sin ta gudanar a sabon zamani. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani sau da yawa ga duniya game da manufar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, da ra’ayin Sin na sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, kana kasar Sin mai bude kofa za ta kara samar da dama ga duniya wajen samun ci gaba.
A shekarar 2022, yawan kudin shige da ficen kayayyaki na kasar Sin ya zarce kudin Sin Yuan triliyan 40 a karo na farko, inda ta kiyaye matsayinta na kasa ta farko da ta fi yin cinikin kaya a duniya a shekaru 6 a jere. Wannan ya shaida cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje.
A ranar 18 ga watan Nuwanba na shekarar 2022, shugaba Xi Jinping ya bayyana a gun taron karba-karba na shugabannin kungiyar APEC cewa, a shekarar 2023, Sin za ta yi la’akari da gudanar taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa na kasashe masu bin shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3, don samar da gudummawa wajen samun ci gaba da wadata a yankin Asiya da tekun Pasifik da duk duniya baki daya.
A gun bikin baje koli na kayayyakin da ake shigar da su kasar Sin karo na 5, shugaba Xi Jinping ya kara bayyana manufar Sin ta fadada bude kofa ga kasashen waje don samar da damar raya tattalin arzikin duniya ta bude kofa.
Bisa rahoton bude kofa na duniya na shekarar 2022 da aka gabatar, Sin ta samu nasarori wajen bude kofa ga kasashen waje, inda ta kasance kasa mai muhimmanci wajen sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya, kana ta sauke nauyin dake wuyanta na gabatar da damarmakin kasuwanni ga duniya da kuma sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya. (Mai Fassara: Bilkisu Xin da Zainab Zhang)