A baya-bayan nan, kungiyar kasashen musulmi (OIC), ta gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Yaounde na kasar Kamaru.
Yayin taron, an tattauna kan ci gaban da aka samu a hadin gwiwar Sin da kungiyar OIC a shekarun baya-bayan nan. Don gane da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta bayyana a yau, yayin taron manema labarai da aka saba yi kullum cewa, Sin da kasashen musulmi dadaddun abokai ne. Ta ce bangarorin biyu sun goyi bayan juna wajen kare muradunsu, da hada hannu wajen ganin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta haifar da kyawawan sakamako.
Ta kara da cewa, Sin ta shirya ci gaba da hada hannu da kasashen musulmi wajen aiwatar da shawarar samar da ci gaba a duniya da ta tsaron duniya da ta cudanyar mabambantan al’adu, tare da hada hannu wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa a duniya. (Fa’iza Mustapha)