Kasar Sin ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba na kare hakkoki da muradunta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ce ta bayyana haka, inda ta ce Sin ta yi imanin cewa, kariyyar cinikayya ba hanya ce mai bullewa ba, kuma babu mai cin nasara a yakin cinikayya ko na haraji. Tana mai cewa wannan batu ne da kasa da kasa suka amince da shi.
- Rashin Haɗin Kai Na Barazana Ga Makomar Arewa – Sarkin Zazzau
- Cutar Sanƙarau Ta Kashe Mutum 26, 248 Sun Kamu A Kebbi
Mao Ning na bayyana haka a yayin da take mayar da martani ga tambayar da aka mata game da matakin shugaban Amurka na sanya karin harajin kaso 25 kan kayayyakin karafa da goran ruwa dake shiga kasarsa.
Da take tsokaci game da shirin Ukraine na amincewa da tayin Amurka na tsagaita bude wuta tsawon kwanaki 30, biyo bayan tattaunawar da ake yi a birnin Jeddah na Saudiyya, Mao Ning ta ce fatan kasar Sin ita ce, dukkan bangarori masu ruwa da tsaki su tattauna tare da cimma yarjejeniyar da samar da mafita mai dorewa da za ta yi la’akari da damuwar kowanne bangare. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp