An zabo kayayyakin da za a gabatar yayin faretin soja na kasar Sin da za a yi ranar 3 ga watan Satumba ne daga kayyayakin ayyukan soja na yau da kullum, wadanda aka kera a cikin gida, inda za a gabatar da mafi yawa daga cikinsu ga al’umma a karon farko.
An bayyana haka ne yayin taron manema labarai da aka yi yau Laraba game da shirye shiryen gudanar da faretin na ranar 3 ga watan Satumba, albarkacin cika shekaru 80 da samun nasarar turjewa harin Japan da yakin duniya na II.
- Hukumar ‘Yansanda Ta Yi Watsi Ga Ƙarin Girma Ga ASP 179, Ta Ɗaga Darajar 952 Zuwa DSP
- CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Nairobi
Wu Zeke, babban jami’in sashen rundunar hadin gwiwa na hukumar tsakiya mai kula da harkokin sojin kasar Sin, ya ce faretin zai kunshi gabatar da kayayyakin yaki kirar kasar Sin kadai, kuma zai kasance karo na farko da Sin za ta gabatar da sabbin makamai masu yawa na runudnar sojinta(PLA), tun bayan wanda aka yi a ranar bikin kafuwar kasar a shekarar 2019.
Makaman za su nuna ci gaban da aka samu a fannin fasahar sadarwa, tare da nuna karfin rundunar ta rungumar ci gaban fasaha da sauyin tsarin yaki, domin samun nasara idan bukatar hakan ta taso.
Ya kara da cewa, faretin na ranar 3 ga watan Satumba zai kasance irinsa na farko da za a yi bayan kasar Sin ta hau sabon tafarkin inganta zamanantar da kanta a dukkan fannoni. (Fa’iza Mustpha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp