Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba yi a ranar 14 ga wata cewa, daga yau Laraba 15 ga watan Maris, kasar Sin za ta kara yawan jirage don yin tafiye-tafiye zuwa ketare ga ‘yan kasar, domin kara samar da yanayi mai kyau ga harkokin yawon bude ido.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, a baya-bayan nan, bangaren kasar Sin ya dawo da zirga-zirgar jiragen sama ga ‘yan kasar Sin a wasu kasashe, kuma ana aiwatar da shi yadda ya kamata.
Kwanan nan, yanayin da ake ciki game da annobar COVID-19 a kasar Sin ya daidaita, kana bukatar jama’a na yin tafiye-tafiye zuwa waje ya karu matuka, kasashe da dama na sa ran zuwan Sinawa masu sha’awar yawon bude ido.
Don haka, kasar Sin ta yanke shawarwarin da suka dace, kuma hukumomin da lamrin ya shafa, za su ci gaba da jagorantar kamfanonin yawon shakatawa, don tsarawa da aiwatar da su kamar yadda aka tsara. (Safiyah Ma)