Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta yi karin haske kan shirin tattauna batun kamfanin TikTok a ganawar da tawagogin Sin da Amurka za su yi a kasar Sifaniya a gobe Lahadi, 14 ga wata.
Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, matsayin kasar Sin kan batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma bai taba canzawa ba. Ta ce kasar Sin tana da cikakkiyar niyyar kare hakkin kamfanoninta, kuma za ta tantance batun kamfanin TikTok bisa doka. Ban da haka, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan ikon kebanta bayanai da tabbatar da tsaronsu, ba za ta taba bukatar wani kamfani ya tattara bayanai a sauran kasashe ta wata haramtacciyar hanya ba.
Sanarwar ta kara da cewa, bisa la’akari da yadda tawagogin kasashen Sin da Amurka za su tattauna maganar TikTok da sauran batutuwa, kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka da ya hada hannu da bangaren Sin, don nemo bakin zaren warware matsalar da ake fuskanta, da samar da muhalli mai adalci ga kamfanonin Sin dake gudanar da harkokinsu a kasar Amurka, ciki har da TikTok, ta yadda za a tabbatar da ci gaban huldar cinikayya a tsakanin kasashen 2, cikin wani yanayi mai inganci da dorewa. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp