Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, nan ba da jimawa ba kasar Sin za ta gudanar da taron mata na duniya a birnin Beijing a daidai lokacin da ake cika shekaru 30 da gudanar da babban taron mata na duniya a shekarar 1995. Ya ce, kasar ta Sin tana son yin aiki kafada da kafada da dukkan kasashen duniya don kara hanzarta aiwatar da sabon tsarin ciyar da mata gaba a dukkan fannoni, da kuma rubuta wani sabon babi na raya al’amuran mata a duniya.
Guo ya ce, ta fuskar abin da aka sa gaba a duniya, akwai sauran shekaru biyar kafin a cimma muradun samar da ci gaba mai dorewa na shekarar 2030. Batun ciyar da mata gaba a duniya yana fuskantar dimbin kalubale masu tsanani yayin da kuma a lokaci guda hakan ke kawo damammaki masu yawa. A fannin inganta daidaito tsakanin jinsi da ci gaban mata a dukkan fannoni, kasar Sin ba mai neman tabbatar da hakan ne kawai ba, har ma ta kasance mai yi a aikace.
Guo ya kuma bayyana cewa, tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18, harkokin mata na kasar Sin sun samu bunkasa, da samun nasarori masu dimbin tarihi, da yin gyare-gyare a dukkan fannoni. Hanyar ci gaban mata a karkashin tsarin gurguzu mai kunshe da sigogin kasar Sin ta nuna matukar samun kuzari da fa’ida ta musamman. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp