Kwamitin tsara ka’idojin buga harajin kwastam, na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya bullo da wani kudurin dake cewa, bisa sanarwar soke buga harajin kwastam kan kaso 98%, na hajojin kasashe masu karancin ci gaba da kwamitin ya fitar, kana kuma bisa takardun bayanin da aka yi musayar su tsakanin gwamnatin kasar Sin da wasu kasashe, tun daga ranar 25 ga watan Disambar shekara ta 2023, Sin za ta soke buga harajin kwastam kan kaso 98% na hajojin wasu kasashen Afirka shida, ciki har da Angola, da Gambiya, da Kongo(Kinshasa), da Madagascar, da Mali, da kuma Mauritaniya.
Wannan rangwame da kasar Sin ta baiwa wadannan kasashe shida, zai taimaka ga karfafa hadin-gwiwa, da sada zumunta tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, tare kuma da raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin bangarorin biyu. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da samar da irin wannan gata ga daukacin kasashe masu karancin ci gaba, da suka kulla dangantakar diflomasiyya da ita. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp