Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jaddada cewa, kumbo maras matuki na ayyukan farar hula na Sin, wanda ya shiga samaniyar Amurka bisa kuskure, kuma matakin harbo shi da Amurka ta dauka, amfani ne da karfin tuwo, da wuce gona da iri, matakin da ko alama Sin ba za ta amince da shi ba.
Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce cikin tsawon lokaci, Amurka ta sha amfani da fasahohin zamani ta hanyoyin da suka sabawa ka’ida, tana aiwatar da manyan ayyukan leken asiri, da satar bayanan sirri a dukkanin sassan duniya, ciki har da na kawayen ta, wanda hakan ya keta ‘yancin mulki da moriyar kasashen, kana matakin ya gurgunta dokokin kasa da kasa, da ka’idojin cudanyar kasa da kasa.
Jami’in ya kara da cewa, Amurka kasa ce dake kan gaba a duniya baki daya, wajen leken asiri da sanya ido, ta amfani da na’urorin zamani. (Saminu Alhassa)