A gun taron kwamiti mai kula da harkokin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 57 da aka gudanar a jiya Talata, kasashe fiye da dari sun gabatar da jawabi cikin hadin gwiwa ko kuma su kadai, don bayyana goyon bayansu ga matsayi mai adalci da Sin take dauka tare da yaki da siyasantar da batun hakkin dan adama. Wannan wani martani ne game da maganar da wasu kasashe, ciki har da Amurka suke yi na kai hari kan halin da Sin take ciki ta fuskar hakkin dan Adam.
Tawagar wakilan Sin ta yi jawabi kan ainihin halin da Sin take ciki na kare hakkin dan Adam, tare da fayyace laifuffukan da wasu kasashe, ciki har da Amurka suke gudanarwa na keta hakkin, tare kuma da kalubalantar wadannan kasashe da su dauki matakan da suka dace don kare hakkin, da ma taka rawa a sha’anin kare hakkin dan adam a duniya. (Amina Xu)