An gabatar da muryoyin kasashe masu tasowa a yayin taron tsaro na Munich na bana (MSC), inda mahalarta taron suka yi kira da a samar da tsari na kasa da kasa da ke nuna hadin kai da samun nasara tare.
A wani taron tattaunawa mai taken “Sake fasalin alkiblar da ake bi: hadin gwiwa tsakanin kasashe masu ci gaba da masu tasowa”, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya bayyana cewa, sakamakon matsaloli na baya-bayan nan kamar COVID-19 da rikicin Rasha da Ukraine ya nuna rashin hadin kai da aka fama da shi.
Akufo-Addo ya ba da misali da yadda wasu kasashen yammacin duniya ke nuna rashin son taimakawa yayin da Afirka ke neman allurar rigakafin COVID-19 ruwa a jallo. Shugaba Akufo-Addo ya ce, “Wannan misali daya ne na rashin hadin kai. Don haka, muna bukatar hadin kai na hakika tsakanin kasashen da suka ci gaba da masu tasowa”.
Yayin da yake karin haske kan masu goyon bayan kasashe masu tasowa, ministan harkokin wajen kasar Togo Robert Dussey ya bayyana cewa, kasar Sin na daya daga cikin kasashen da ke goyon bayan bunkasuwar tattalin arzikin da inganta harkokin sufurin kasashen Afirka. (Mai fassarawa: Ibrahim)