Tun bayan da kasar Sin ta daidaita matakanta na yaki da annobar COVID-19, kasashe a fadin duniya ke murna da farin ciki, tare da maraba da miliyoyin Sinawa dake fatan kawo ziyarar yawon bude ido da ma kasuwanci a kasashensu.
Sassauta dokar takaita tafiye-tafiyen da ta fara aiki tun a ranar 8 ga watan Janairu, bayan tsawon shekaru 3 da barkewar annobar da ta addabi sassan duniya, na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Sinawa a fadin duniya ke shirin bikin bazara ta sabuwar shekarar Zomo bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Inda ake sa ran Sinawa za su yi biliyoyin tafiye-tafiye a cikin gida da ma kasashen waje, yayin bikin na kwanaki 7 da za a fara daga ranar 21 ga wata.
Saboda girman kasuwar kasar Sin, ya sa kasashe da yankuna na duniya, bayan samun wannan albishir, suka fara jan hankalin Sinawa, ta hanyar wallafa hotuna da bidiyon fitattun wuraren yawon shakatawa dake kasashensu a shafin Weibo.
Sai dai yayin da wasu kasashe ke murna da wannan mataki na kasar Sin, wasu kasashen yammacin duniya na neman siyasantar da matakan kamar yadda suka saba. Hali aka ce zanen dutse.
Masu fashin baki na cewa, matakin na kasar Sin zai ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya, wanda ya fuskanci koma baya, sakamakon tasirin annobar COVOID-19. Wannan ne ma ya sa hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bukaci kasashen duniya, da su martaba matakai na kimiyya wajen yaki da wannan cuta, maimako nuna yatsa ga wata kasa da nufin mayar da hannun agogo baya, a kokarin da ake yi na ganin bayan wannan cuta.
Masu sharhi na cewa, abubuwan da suka faru a duniyar bil-Adama tsawon wadannan shekaru uku sanadiyar tasirin wannan annoba, ya ishi mai hankali darasi. Kukan kurciya dai jawabi ne, amma mai hankali ne kadai ke ganewa.