A yayin taron manema labaru da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar a yau, wani dan jarida ya yi tambaya cewa, a kwanakin baya, an bude taron koli na shugabannin Amurka da Afirka a birnin Washington dake kasar Amurka.
Manyan jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana ra’ayoyin da ba su dace ba game da kasar Sin. Mene ne ra’ayin kasar Sin kan wannan batu?
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, tallafawa ci gaban Afirka, nauyi ne da ya rataya a wuyan kasashen duniya baki daya, kuma yana fatan Amurka za ta dubi hadin gwiwar Sin da Afirka da idon basira.
Kasashen Afirka da jama’arsu suna da hikima da basirar zaben abokan hadin gwiwa da suka dace da moriyarsu. Haka kuma, kasashen Afirka da jama’arsu, sun fi kowa sanin wanda yake kaunarsu a zahiri. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp