Kasashe a fadin duniya, musamman na yankin kudu maso gabashin Asiya, na murna dangane da tsammanin miliyoyin Sinawa masu tafiye-tafiye, bayan dage dokar takaita tafiye-tafiye a kasar.
A jiya Lahadi, 8 ga wata ne aka dage dokar takaita tafiye-tafiyen da aka ayyana shekaru 3 da suka gabata a kasar Sin biyo bayan barkewar annobar COVID-19. Sassauta dokar na zuwa ne a daidai lokacin da bikin bazara ta sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin ke karatowa. Akwai yuwuwar Sinawa za su yi biliyoyin tafiye-tafiye a cikin gida da ma kasashen waje, yayin bikin na kwanaki 7 da za a fara daga ranar 21 ga wata.
Sauyin matakan yaki da cutar dai ya samu matukar karbuwa daga kasashe da dama, ciki har da Thailand, da Malaysia, da Singapore, da Cambodia, da Indonesia, da Philippines, da New Zealand, kasashen dake matukar dokin karbar bakuncin Sinawa masu yawon shakatawa.
Hukumomin lura da fannin yawon bude ido a Thailand, sun ce kasar ta shirya tsaf domin karbar baki Sinawa, kuma suna fatan adadin Sinawa ’yan yawon shakatawa da kasar za ta karba a bana kadai, zai kai mutum a kalla miliyan 5, adadin da ya kai kusan rabin Sinawa miliyan 11.5 da suka ziyarci kasar a shekarar 2019.
Gwamnatoci a fadin duniya ba su tsaya bata lokaci ba wajen jan hankalin Sinawa matafiya saboda sassauta dokar a jiya, inda suka yi ta wallafa hotuna da bidiyon fitattun wuraren yawon shakatawa a shafin Weibo, wanda yake tamkar shafin Twitter a kasar Sin.
Bayanai sun bayyana cewa, gangamin jan hankalin matafiya ya zo a kan gaba, bisa la’akari da karuwar bukatar tafiye-tafiye saboda zuwan bikin bazara. (Fa’iza Mustapha, Saminu Alhassan)