Baje kolin mutum-mutumin inji na duniya ko WRC a takaice, da aka gudanar a cibiyar bunkasa fasahar kere-kere cikin sauri ko E-Town na birnin Beijing, wato taron shekara-shekara na kamfanonin kasar Sin da na kasashen waje don yin cudanya da juna, da tattaunawa kan yiwuwar hadin gwiwa, da musayar ra’ayi kan ci gaba da aka samu a fannin kirkire-kirkire da fasahar kera mutum-mutumin inji. Ya jawo hankulan duniya yayin da kasashen duniya ke kara sha’awar yin hadin gwiwa da kasar Sin sakamakon wannan taro, wanda ke wakiltar kudurin kasar Sin na zama jagorar duniya a fannin fasahar kera mutum-mutumin inji.
- Sin Ta Fara Aiwatar Da Manufar Rangwame Domin Bunkasa Cinikayyar Musayar Kayayyakin Amfani A Gidaje
- Li Qiang Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Don Bunkasa Masana’antar Mutum-Mutumin Inji
Kamfanoni 169 ne suka baje kolin sabbin samfuran kirkire-kirkire sama da 600 daga duk fadin duniya a bikin mai taken “Sa kaimi ga raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko tare, don kyakkyawar makomar fasahar zamani ta bai daya”, wanda ya hallara masu bincike, da shuwagabannin masana’antu, da masu sha’awar bincike don kara fahimtar fasahar mutum-mutumi inji. Baje kolin ya gudana ne tsakanin ranakun 21 zuwa ta 25 ga Agusta, wanda ya haskaka karfin kasar Sin kan kirkire-kirkire da fasahar kera mutum-mutumi, tare da samar da sabbin hanyoyin yin musayar kwarewa da ilimi, da ingiza sha’awar juna a fannin kirkire-kirkire da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a masana’antar sarrafa mutum-mutumin inji.
Amfanin da sabbi kuma manyan fasahohi kamar su fasahar mutum-mutumin inji da kasar Sin ke yi wajen bunkasa sassan tattalin arziki da dama, ya samu ci gaba a baya-bayan nan, saboda yunkurin da ake yi na bunkasa fannin fasahar kirkire-kirkire, da habaka masana’antu. Kazalika, sakamakon ingantacciyar tsarin samar da kayayyaki, da kyakkyawar tsarin amfani da manyan bayanai na kwamfuta, da kyawawan manufofi, darajar ma’aunin masana’antu na bangaren sarrafa mutum-mutumin inji ya tashi zuwa dala miliyan 549 a shekarar 2023, wato karuwar kashi 85.7 cikin dari bisa na shekerar da ta gabata.
Yawan na’urorin mutum-mutumin inji da masana’antun kasar Sin suka samar ya kai tari 430,000 a shekarar 2023, kuma a cikin shekaru ukun da suka gabata, sabbin mutum-mutumin inji da aka hada sun zarce rabin adadi na kasuwannin duniya. Mutum-mutumin inji masu gudanar da ayyuka a masana’antu suna kara habaka masana’antun kasar Sin ta hanyar rage farashi da saurin kirkirar kayayyaki masu inganci. Kuma suna taimakawa ingancin ayyuka a masana’antu cikin aminci. (Mohammed Yahaya)