Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu a majalisar dattawa, Ibrahim Bomai, ya bayar da tallafin kudi naira miliyan 20, barguna 5,000, yadudduka 5,000 da tufafin yara 5,000 ga wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a mazabarsa.
Kayayyakin da tsabar kudi, a cewar shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da babban birnin tarayya, za a raba su ne a gunduma biyar na mazabarsa inda kowannensu zai samu tsabar kudi naira miliyan 4, barguna 1,000, yadudduka 100 da tufafin yara 100.
- Kasashen Duniya Sun Halarci Baje Kolin Mutum-mutumin Inji Na Duniya
- Da Dumi-dumi: Tinubu Ya Maye Gurbin Bichi Da Ajayi A Matsayin Shugaban DSS
Kwamitin da aka kafa domin raba kayayyakin a karkashin jagorancin Alhaji Idi Jugujugu ya fara aikin kai kayan agajin ga mutanen da iftila’in ambaliyar ruwan ya shafa a unguwannin Chukuriwa, Nangere, Yarimaram, Dogo Nini, da Bare-bari Bauwalailai.
Sanata Bomai ya jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon ambaliyar ruwan.