A watan Satumba na shekarar 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarar samun bunkasuwar duniya bisa taken “yadda za a samu bunkasuwar duniya da salon bunkasuwar da ake fatan samu a duniya”. A cikin sama da shekara daya, kasa da kasa sun nuna goyon baya ga wannan shawara.
Ya zuwa yanzu, kasashe fiye da 100 da kungiyoyin kasa da kasa da dama ciki har da MDD, sun nuna goyon baya ga shawarar, kana kasashe fiye da 60 sun shiga rukunin hadin gwiwa na raya shawarar samun bunkasuwar duniya.
Babban sakataren MDD António Guterres ya nuna yabo ga kasar Sin kan muhimmiyar rawar da ta taka wajen goyon bayan ra’ayin bangarori daban daban, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da samun bunkasuwa mai dorewa.
MDD ta nuna goyon baya ga shawarar raya duniya, tana mai imanin cewa, shawarar za ta taimaka wajen raya ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030.
Tsohon firaministan kasar Togo kuma shugaban asusun raya aikin noma na kasa da kasa Gilbert Houngbo ya yi nuni da cewa, asusun ya yaba da aikin yaki da talauci, da tabbatar da samun isasshen abinci, da samar da kudade domin samun bunkasuwa, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da sauransu da aka sanya cikin shawarar samun bunkasuwar duniya.
Kana yana fatan bisa shawarar da burin samun bunkasuwa mai dorewa, kasashen duniya da yankuna za su gudanar da shawarwari da hadin gwiwa mafi dacewa. (Zainab)