Yanzu haka ana gudanar da manyan taruka biyu na kasar Sin wato babban taron majalisar wakilan jama’ar kasar da babban taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar, wannan shi ne karo na farko da aka kira tarukan biyu, tun bayan da da aka kammala babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a shekarar bara, inda aka fi mai da hankali kan yadda za a ingiza aikin zamanintarwa irin na kasar Sin.
A jiya Lahadi 5 ga wata ne, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da rahoton aikinta na shekarar 2023 ga babban taron wakilan jama’ar kasar, inda aka jaddada cewa, gwamnatin kasar za ta ci gaba da nacewa kan manufar raya kasa cikin lumana, ta hanyar kyautata aikin raya tattalin arzikin kasar daga duk fannoni, ta yadda za a cimma burin karuwar tattalin arziki a kasar ta Sin. Kana an yi tsokaci cewa, tabbatar da ci gaban kasar mai inganci, muhimmin bangare ne na zamanintarwa irin na kasar Sin.
Haka zalika, ana sa ran cewa, karuwar GDPn kasar Sin za ta kai kaso 5 bisa 100 a shekarar bana, saboda sabon hasashen da asusun IMF ya yi ya nuna cewa, karuwar tattalin arzikin duniya a bana za ta kai kaso 2.9 bisa dari, adadin da ya ragu da kaso 0.5 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2022. Ban da haka sauran kasashen duniya suna kara nuna imani kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, inda wasu hukumomin kasa da kasa ma suka daga hasashensu kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a cikin ‘yan kwanakin nan.
A sa’i daya kuma, rahoton aikin gwamnatin ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga ketare, lamarin da ya kara imanin ‘yan kasuwan kasashen waje, inda suka tsai da kudurin shiga kasuwar kasar Sin, matakan da aka ambata a cikin rahoton, za su samar da karin damammaki da hidimomi masu inganci ga ‘yan kasuwan ketare. (Mai fassarawa: Jamila)