Kasashen Sin da Rasha da Iran sun yi kira tare da a kawo karshen matakan kakaba takunkumi na bangare daya wadanda ba bisa ka’ida ba, bayan da manyan jami’an diflomasiyyar kasashen uku suka hallara yau Juma’a a birnin Beijing don tattaunawa kan batun nukiliyar Teheran.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu ya jagoranci taron, wanda kuma ya samu halartar mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Ryabkov Sergey Alexeevich da mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi.
- Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
- Wata Rana Za A Yi Wa Gwamnatin Tinubu Sambarka – Minista
Ya kamata bangarorin da abin ya shafa su yi kokarin kawar da musabbabin halin da ake ciki tare da yin watsi da duk wani matsin lamba na takunkumi da kuma barazanar tilastawa, kamar yadda Ma ya bayyana a taron manema labarai da aka gudanar bayan taron.
Yana mai cewa, kasashen uku sun jaddada mahimmancin kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 tsakanin Iran da kasashen duniya masu karfin iko. Inda Iran ta rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar da aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA), tare da manyan kasashen duniya shida a watan Yulin 2015, inda suka amince da takaita shirinta na nukiliya a madadin dage takunkumai. Sai dai a wa’adin farko na Trump, Amurka ta fice daga yarjejeniyar a watan Mayun 2018 tare da maido da takunkuman da ta kakaba mata, lamarin da ya sa Iran ta janye wasu alkawurran da ta dauka na rage karfinta na nukiliya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp