Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da tura wata tawaga ta musamman zuwa jihar Edo domin tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa tare da tabbatar da adalci ga mafarauta matafiya wadanda gungun ‘yan sakai suka kashe a ranar Alhamis a yankin Uromi na jihar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, gwamnatin ta bayyana takaicinta kan lamarin mara dadi da ya haifar da damuwa ga gwamnati da mutanen jihar.
- Tawagar Ma’aikatan Ceto Ta Kasar Sin Ta Isa Birnin Yangon Na Kasar Myanmar
- Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Fiji: Ya Kamata A Koyi Fasahohin Da Kasar Sin Ta Samu A Fannin Raya Kasa
A cewar sanarwar, tawagar za ta tuntubi gwamnatin jihar Edo domin zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da hada kai kan kokarin gurfanar da su a gaban mai shari’a.
Bugu da kari, tawagar za ta gana da shugabannin al’ummar Hausawa na jihar domin tattauna lamarin tare da bayar da shawarwarin da suka dace.
Sanarwar ta bukaci ‘yan jihar da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma, tare da tabbatar wa jama’a cewa, ana daukar matakan da suka dace na diflomasiyya da na shari’a don magance lamarin yadda ya kamata.
Gwamnatin jihar Kano ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da yin addu’ar Allah ya jikansu da rahama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp