Bisa wani bincke da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa, a yayin da akasarin ‘yan Nijeriya ke ci gaba da fama da mastin tattain aziki wanda hakan ya sa samun da suke yi ya ragu, hakan ya nuna yadda ake ci gaba da samun karin yawan ababen hawa da ba a yi masu inshora ba, wadanda suka karu zuwa kimanin miliyan tara.
Kazalika, wasu bayanai da aka samu daga gun hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) da kuma kungiyar da ke yin inshora ta kasa (NIA) sun nuna cewa, akwai ababen hawa da da ke amfanin da tituna kasar nan, wadanda yawansu ya kai miliyan 12, amma miliyan 3.11 kacal ne aka yiwa inshora a karshen 2023, wanda wannan adadin ke nuna cewa, kashi 25 ne kacal a yanzu aka yiwa inshore.
- ‘Yan Bindiga Sun Tarwatsa Kauyuka 10 A Jihar Kaduna
- Talauci Da Rashin Aikin Yi Ne Silar Matsalar Tsaro A Arewa – Dan Masani
Bugu da kari, ana kuma hasashen wannan adadin na ababen hawan da aka yiwa ishorar, mai yuwa zai ragu a 2024.
Yawan adadin ababen hawan da aka yiwa inshora a 2022, ya karu daga miliyan 3.70, inda kuma a 2023 ya karu zuwa miliyan 3.11.
Wannan adadin ya nuna cewa, kimanin ababen hawa 600,000 ne suka ki sabunta inshorar ababen hawansu, musaamman saboda sauyawar yanayin kasuwanci da kuma karuwar ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa, wanda hakan ya sanya masu ababen hawan yin watsi da yin sabunta yin inshorar ababen hawansu.
Har ila yau, karin farashin man fetur da tashin farashin kayan gyran ababen hawa, hakan ya tilasta wasu masu motoci ko dai sun sayar da motocin na su, ko kuma sun aje su a gidajen su ba sa hawansu, inda suke ganin babu wani dalilin da zai sa su yi wa motocin na su inshora.
Kazalika, bisa binciken da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa, wasu daga cikin wadanan ababen hawan miliyan tara da ba yi masu inshora ta ainahi ba, wasu masu ababen hawan na yin amfani da takardun jabu a matsayin sun yiwa ababen hawan na su inshora.
Hatta wasu masu ababen hawan da ba su yiwa ababen hawansu inshora ba, wasun su kuma da suke da takardun hakakika na inshorar a baya, sun gaza sake sabunta takardun na sun a inshore bayan tuni, takardun na su, aikinsu ya kare.
Bisa tsarin dokar hukumar, ta bukaci dukkan wata motoci na tsari na uku da ke bin tituna kasar nan, dole ne su bi tsarin yin inshorar ababen hawan su, ko kuma su yi cikakkiyar inshora data kai kashi 10 a cikin dari.
Har ila yau, motoci na tsari na ukun, farashinsu na yin inshora, an kayade kan Naira 15, 000, sabanin yadda a shekarar da ta wauce ake biyan Naira 5,000 don a rage hauhawan farashi da kuma tsadar kayan gyran ababen hawa.
Bugu da kari, binciken ya nuna cewa, akasarin direbobi sun gwammace su yi inshora ta jabu saboda ta fi rahusa don su gujewa kamun jami’an tsaro, ganin cewa, ba su da cikakken ilimi na sanin alfanun takardun inshora na ainahi.