Hukumar UNICEF ta ce akalla kashi 57 na yaran da ke kasa da shekara biyar a Jihar Kano, na fama da rashin girman jiki sakamakon illar da karancin abinci mai gina jiki ya musu.
Shugaban sashen kula da bangaren abinci mai gina jiki na UNICEF da ke Kano, Oluniyi Oyedokun ne, ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da jawabi wajen wani taron masu ruwa da tsaki kan inganta lafiyar mata masu juna biyu.
- An Kaddamar Da Dandalin Bunkasa Noma Da Yaki Da Fatara Na Sin Da Afirka A Kenya
- Ambaliyar Ruwa: Mutane 16 Sun Rasu, 3,936 Sun Rasa Matsugunansu A Jigawa – SEMA
Ya ce daga cikin kowane yara guda biyu da aka gani, daya na fama da wannan matsalar a Kano.
Oyedokun ya kara da cewar Gidauniyar Bill da Malinda na daukar nauyin shirin bayar da tallafi ga wadannan yara a jihohi biyar da ke cin gajiyar sa cikinsu har da Kano.
Ya kuma kara da cewar alkaluman hukumar sun nuna cewar kashi sama da 60 na matan da ke yankin Arewa Maso Yamma na fama da rashin kwayoyin halittar jinin da ke sarrafa iska a cikin jininsu.
Oyedokun, ya bayyana fatansa na ganin Jihar Kano, ta zama ta farko da za ta bayar da nata gudunmawar domin aiwatar da asusun tallafawa yaran da suke fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki.