A yau, rukunin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa na kasar Sin kashi na biyu wadda za ta je yankin Abyei, ya tashi daga birnin Zhengzhou na kasar Sin, da jirgin saman soja domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 12. Bugu da kari, ana shirin tura rukuni na biyu na tawagar a tsakiyar watan Mayu.
Kasar Sin ta aike da tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa ta farko zuwa yankin Abyei a watan Mayun shekarar 2024. Tawagar tana dauke da bangarori da dama da suka hada da bangaren tuki, sadarwa, bincike, da kiwon lafiya, wadanda ke yin sintiri da makamai, da kula da wadanda suka jikkata, da kuma masu rakiya daga nesa. Bayan kammala mika ragamar aiki, kashi na farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa da aka aika zuwa Abyei za su koma kasarsu nan gaba kadan. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp