Kashin karshe na Mahajjatan jihar Kwara da suka yi aikin hajjin bana a kasar Saudiyya sun iso Ilorin a sanyin safiyar Laraba.
Alhazan 328 sun sauka filin jirgin sama na Ilorin a cikin jirgin Max Air da karfe 1:17 na dare.
Mahajjatan sun dawo ne tare da dukkan jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kwara, ciki har da shugaban kungiyar, Dr Abdulkadir Sambaki.
Dukkanin mahajjatan da suke cikin farin ciki sun samu tarba daga iyalai da ’yan uwansu, wadanda suka kwana a filin jirgin domin tarbar maniyyatan da suka dawo gida daga kasa mai tsarki.
Biyu daga cikin mahajjatan da suka zanta da LEADERSHIP, Alhaja Sherifat Shade AbdulKareem ma’aikaciyar The Herald Newspapers, da Alhaja Ramata Bukola Olesin ta ma’aikatar ilimi ta Ilorin, sun godewa Allah da ya ba su damar gudanar da aikin hajjin na bana.