Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar nazarin watsa labaran kasa da kasa a sabon zamani ta tattara a kwanakin baya, karkashin jagorancin kafar talabijin ta CGTN, dake karkashin rukunin kafofin watsa labarai na kasar Sin CMG, da jami’ar Renmin ta kasar Sin, ya nuna cewa, wadanda suka bayyana ra’ayinsu ‘yan asalin kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, kaso 93.8 bisa dari sun yaba matuka da babban sakamakon da aka samu, yayin gina shawarar a cikin shekaru goma da suka gabata.
A cikin wadannan shekaru goma, sabbin manyan kayayyakin more rayuwar jama’a da aka gina sun kyautata rayuwarsu a bayyane, kuma wadanda suka bayyana ra’ayinsu daga kasashen da suka shiga shawarar, kaso 86.9 bisa dari suna ganin cewa, manyan kayayyakin more rayuwar jama’a na kasashensu sun kyautata matuka, kuma suna amfanar al’ummun kasashen yadda ya kamata.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Zai Halarci Bikin Bude Taron BRF
- An Bude Baje Kolin Canton Karo Na 134 A Guangzhou
Yayin kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka kada, an lura cewa, matakin da kasar Sin ta dauka na rage, ko soke basusukan da take bin kasashen da suka shiga shawarar ya fi samun amincewa daga wadanda suka bayyana ra’ayin. Daga cikinsu, kaso 83 bisa dari na ganin cewa, matakin da kasar Sin ta dauka ya shaida cewa, kasar tana sauke nauyin dake wuyanta, a fannin taka rawar gani ga ci gaban yankuna masu karancin wadata.
Rahotannin sun bayyana cewa, an gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ne ga mutane 3,857 dake kasashe 35, wadanda suka kunshi Serbia, da Hungary, da Afirka ta kudu, da Agentina, da Saudi Arabiya, da Najeriya, da Brazil, da sauran kasashen da suka shiga shawarar, wadanda suka kai matsayin ci gaba iri daban daban. (Mai fassara: Jamila)