Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin madam Mao Ning, ta bayyana matsayin kasar Sin a fannin tinkarar rikicin Gaza, yayin wani taron manema labaru da ya gudana a yau Litinin, inda ta ce kasar Sin na sa lura kan yanayin da ake ciki tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, tare da fatan ganin an tsagaita bude wuta, da kare fararen hula. A cewarta, kasar Sin na son ganin manyan kasashe su nuna adalci, da kai zuciya nesa, yayin da suke kula da harkokin kasa da kasa.
Ban da haka, jami’ar ta kara da cewa, manzon musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da batun Gabas ta tsakiya, mista Zhai Jun, zai tafi yankin Gabas ta tsakiya a wannan makon da muke ciki, inda zai sa kaimi ga yunkurin sasanta yanayin da ake ciki, da tabbatar da damar daidaita rikicin Gaza ta hanyar sulhu.
Haka zalika, Mao Ning ta yi bayani kan rawar da tawagar kasar Sin ta taka, a taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, wanda aka kawo karshensa a ranar 13 ga watan da muke ciki, inda ta ce, an bayyana ra’ayin Sin a fannin kare hakkin dan Adam, da nasarorin da ta samu a wannan bangare, da kokarin samar da gudunmowa a fannin daidaita batun hakkin dan Adam a duniya, gami da neman tabbatar da adalci a duniya a wannan fanni. (Bello Wang)