Kason farko na tallafin gaggawa da Sin ta aike ya isa filin jirgin saman Istambul na kasar Türkiyya. Kayayyakin dai sun hada da tantuna, da barguna, kuma za a yi jigilarsu zuwa yankunan da suka sha fama da girgizar kasar da ta aukawa wasu yankunan kudancin kasar.
Baya ga wannan tallafi, nan gaba kadan, Sin za ta mika karin rukunonin tallafin gaggawa ga kasar, inda ake sa ran za ta aike da tantuna, da na’urorin kiwon lafiya, da motocin kwashe marasa lafiya.
Rahotanni na cewa mummunar girgizar kasar da ta aukawa yankin kudancin Türkiyya da arewacin Syria, ita ce mafi muni da ta auku a yankin cikin kimanin karni guda.
Sakataren ofishin tsare-tsaren ayyukan jin kai da ba da tallafin gaggawa na MDD Martin Griffiths, ya shaidawa manema labarai a lardin Kahramanmaras na Türkiyya cewa, sama da kasashe 100 ne suka aike da tallafin tawagogin ayyukan gaggawa ga Türkiyya, amma duk da haka ana bukatar kari.
Jami’in ya ce MDD za ta kaddamar da gidauniyar neman tallafin kudade, domin hukumomin da za su tallafawa al’ummun da ibtila’in ya shafa.
Kamfanin dillancin labarai na Anadolu dake Türkiyya, ya ce an bude kan iyakar kasar da Armenia a karon farko cikin gwamman shekaru, domin samar da tallafin jin kai ga masu bukata. Kaza lika tawagar Armeniyawa masu aikin jin kai sun shigar da tan 100 na kayan abinci, da magunguna, da ruwan sha cikin lardin Adiyaman na kudu maso gabashin Türkiyya, kamar dai yadda wani sakon tiwita na wakilin musamman na kasar Türkiyya, game da sasanto da Armenia Serdar Kilic ya bayyana. (Saminu Alhassan)