Wang Dongtang, jamii a maaikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana cewa, cinikayyar zamani ta kasar ta samu babban ci gaba a shekarar 2022.
Wang Dongtang ya bayyana haka ne a yayin bikin bude baje kolin cinikayya na zamani karo na biyu a birnin Hangzohu na lardin Zhejiang dake yankin gabashin kasar. Yana mai cewa, a shekarar 2022, darajar cinikayyar hidima ta zamani ta kasar Sin ta karu da kashi 3.4 bisa 100 kan na shekarar 2021, wadda ta kai dalar Amurka biliyan 372.71, karuwa mafi girma a tarihi.
- Ya Zuwa Karshen Shekarar Bara Tsayin Manyan Titunan Mota Na Kasar Sin Ya Kai Kilomita 177,000
- Babban Masallacin Adogba: Sultan Da Makinde Sun Kafa Turbar Kawar Da Bambancin Kabilanci Da Na Addini A Nijeriya
Da yake bayani kan rahoton da aka fitar game da bunkasuwar cinikayyar zamani na kasar a shekarar 2022, Wang ya bayyana cewa, a cikin wannan lokaci, yawan shigi da ficin kayayyaki ta intanet tsakanin kasashe, ya kai yuan triliyan 2.11, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 296.3, wanda ya karu da kashi 9.8 bisa 100, kan makamancin lokaci na shekarar 2021.
Ya ce, hada-hadar cinikayyar zamani ta zama sabon injiniya ga yunkurin kasar Sin na gina kasa mai karfin kasuwanci, da sabon mataki na shirin kara bude kofa. Ya kara da cewa, za a yi kokarin karfafa inganta samfuran kayayyaki, da raya sabbin fasahohin kasuwanci da daidaita dokokin ciniki na zamani tare da ingancin mizanin ma’auni. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)