Kungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta bayyana cewa, bangaren masana’antu a Nijeriya yana kara samun karuwar kashe kudade wanda a yanzu ya kai kashi 30.38 cikin 100 duk shekara, inda ya kai naira tiriliyan 5.34 a farkon shekarar 2024, yayin da kungiyar ta ce mambobinsu sun kashe naira biliyan 238.3 wajen samun wutar lantarki lokcin da ta wutar ta katse a fadin Nijeriya.
Baya ga haka, an samu raguwar karfin sayayyar masu saye da kashi 357.57 cikin 100 na kayayyakin da masana’antu suke sarrafawa zuwa naira tiriliyan 1.24 a rubi’i na biyu na shekarar 2024, idan aka kwatanta da naira biliyan 271 da aka samu a bara.
- Gwamnatin Tarayya Da EU Sun Kulla Yarjejeniyar Bunkasa Wutar Lantarki
- Gwamnatin Kano Ta Koka Kan Yawaitar Satar Magani A Asibiti
Kungiyar MAN ta bayyana hakan ne a cikin binciken tattalin arziki na 2024 da ta fitar a ranar Litinin.
“A bisa ka’ida, abin da masana’antun ke samarwa a Nijeriya ya karu da kashi 30.38 cikin 100 duk shekara, wanda ya kai naira tiriliyan 5.34 a rabin shekarar 2024.
“Wannan ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin cikin gida, kamar yadda aka nuna a cikin kididdigar farashin masu sayan kayayyaki (CPI), wanda ya kai kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin 2024.
“Karin da aka samu a cikin kididdigar ya rufe matsalolin da masana’antun ke fuskanta wajen kiyaye matakan fitarwa na ainihi, yana nuna tasirin hauhawar farashin kayayyaki a fannin,” in ji kungiyar.
A cikin rahoton, MAN ta danganta karuwar da aka samu a kayyakin da ba a sayar da su a kan raguwar karfin sayayyar kayan masarufi, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, cire tallafi, da kuma faduwar darajar naira.