Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano, KEDCO ya ce, ya yi asarar kimanin Naira biliyan 6 sakamakon katsewar wutar lantarki da ta shafe kwanaki 12 wacce ta yi mummunar illa ga harkokin kasuwanci a sassan da yake bai wa wutar da suka hada da jihohin Kano, Jigawa da Katsina.
Ya kara da cewa, a lokacin rashin wutar, an lalata taransfoma 70, lamarin da ya kara dagula wa kamfanin lissafi.
- Ƴansanda Sun Kama Ƴan Ƙasar Waje 130, Da Ake Zargi Da Sata Ta Yanar Gizo
- Yadda Rashin Tsaftar Cikin Gida Ke Haifar Da Kananan Cututtuka
Shugaban sashen sadarwa na kamfanin KEDCO, Sani Bala Sani ya bayyana cewa, kamfanin na iya kokari wurin bayar da fifiko ga rarraba wutar ga masana’antu don tallafawa ci gaban tattalin arziki, musamman a Kano da sauran cibiyar masana’antu.
Katsewar wutar sakamakon lalacewar layin watsa wutar lantarkin mai karfin 330kV, ya katse wasu jihohin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas daga tushen samar da wutar na kasa.