Ƙungiyar kwallon kafa ta Katsina United ta gabatar da sabbin yan wasa biyu Abdullahi Musa da Saidu Adamu waɗanda suka ɗauko daga Kano Pillars a yau Asabar.
Shugaban riƙo na ƙungiyar Kabir Danlami Rimi ne ya gabatar da ƴan wasan a filin wasa na Muhammadu Dikko dake birnin Katsina.
- Dan Kwallon Kano Pillars Ya Zazzaga Kwallaye Biyar A Ragar Gombe United
- Kano Pillars: Yaushe Kungiyoyin Kwallon Nijeriya Za Su Daina Shiga Matsalar Kudi?
Duka sabbin ƴan wasan sun saka kwantiragin shekara ɗaya a Dikko Warriors, Abdullahi mai tsaron baya da Sa’idu mai wasan tsakiya duka tsaffin ƴan wasan abokiyar hamayyar Katsina United, wanda ke nufin cewa kakar wasa mai zuwa zai ƙayatar matuƙa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp