Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirin raba injin Huɗar gona guda 4,000 ga manoma a fadin jihar a wani shiri na inganta rayuwar al’umma.
Shirin wanda gwamnan jihar Dikko Umar Radda ke jagoranta na da nufin bunkasa ayyukan noma da tallafawa noman rani a jihar.
- Xi Jinping: Ana Kokarin Raya Tsibirin Hainan Bisa Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin
- Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa, Sun Ceto Mutane 20 A Katsina
A cewar ko’odinetan kwamitin kula da al’umma a matakin farko (CLC), Dakta Kamualadee Kabir, za kuma a samar da injinan akan tallafin kashi 60 zuwa 70 cikin 100 domin samar da wadatar injunan cikin sauki ga manoma.
Bugu da kari, za kuma a raba injinan ban ruwa domin inganta noman rani a jihar.
Haka kuma za a raba awaki 48,000 ga mata a fadin jihar a wani bangare na shirin, inda kowace unguw za ta samu awaki goma domin inganta rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin mata.
Dokta Kabir ya bukaci masu unguwanni da su lalubo wadanda suka fi cancanta domin cin gajiyar shirin.