Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Kawu Sumaila, ya nemi Shugaban NNPP na Kano, Hashim Dungurawa, ya bayar da hakuri a bainar jama’a kan zargin da ya masa na cin hanci da rashawa.
Lauyan Kawu, Barista Sunusi Musa, ya aika wa Dungurawa wasika tare da ba shi wa’adin sa’o’i 24 ya bayar da hakuri da kuma janye kalamansa.
- Tinubu Zai Tafi Brazil Kwana Biyar Bayan Dawo Wa Daga Saudiya
- Gwamnatin Kano Za Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Hausa – Mataimakin Gwamnan Kano
Dungurawa ya zargi Kawu da cin hanci, magudin zabe, da wasu munanan laifuka a wata hira da ya yi a gidan rediyo. An kuma yada zargin a shafukan sada zumunta.
Daga cikin zarge-zargen, Dungurawa ya ce Kawu ya karkatar da kudade da aka ware don ayyuka a yankinsa, sannan kuma ya karbi kudi domin juya sakamakon zabben gwamnan Kano na 2023.
Lauyan Kawu, ya bayyana cewa wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne kuma sun bata sunan Kawu a matsayin dan siyasa mai gaskiya da amana.
Idan Dungurawa bai bayar da hakuri ba, Kawu ya shirya kai shi kotu, kamar yadda lauyansa ya bayyana.
Har yanzu dai Dungurawa bai mayar da martani kan lamarin ba.