Yayin da ake cika shekaru 104 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar, ya gudanar da wani taron nazari, inda sakatare-janar na kwamitin, kuma shugaban kasar Xi Jinping ya yi kira ga jagoroin jam’iyyar a dukkan matakai da su sauke nauyin da ya rataya wuyansu na tabbatar da jam’iyyar ta ci gaba da jagorantar ragamar shugabanci da tsayawa da kafarta.
Shekaru 104 ba magana ce ta wasa ba, sun nuna jajircewar kasar Sin da jam’iyyar wajen zabarwa kasar hanyoyin samun ci gaba. Mun riga mun san cewa kasar Sin ta yi abun a-zo-a-gani a duniya, na tsayawa kai da fata wajen zabarwa kanta hanya mafi dacewa da ita na samun ci gaba da ingantuwar walwalar al’ummarta.
- An Yi Bikin Kade-Kade Don Taya Murnar Cika Shekaru 104 Da Kafuwar JKS
- Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu
Karkashin jagorancin jam’iyyar, kasar Sin ta yi namijin kokarin kai kanta ga zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, wadda ta riga kowacce fatattakar talauci shekaru 10 kafin lokacin da aka kayyade, ta zama kasar dake ingiza habakar tattalin arzikin duniya, haka kuma ta zama mai ingiza ci gaban sauran kasashe musamman masu tasowa. Idan muka duba bangaren kirkire-kirkire, ba shakka kasar Sin ta zama jagora a duniya, inda take kokarin zama mai dogaro da kanta a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha.
Akwai tarin abubuwa da muka gani na ci gaban kasar Sin da ba za mu iya zayyanawa daya bayan daya ba. Amma kun san dalilin irin wannan ci gaba da kasar Sin ta samu? Shi ne tsayuwar daka wajen jagorantar al’amuranta da kanta. kasar Sin ta yi fafutuka wajen bijirewa mulkin danniya da zama ’yar amshin shata, ta bijiro da nata tsari, wanda take ganin shi ya fi dacewa da al’ummarta, kuma shi din ne ya kai ta ga matsayin da ta kai a yanzu. Wannan ya kara tabbatar mana da abun da Bahaushe ke cewa, “kayan aro baya rufe Katara”.
Bisa kiran da shugaba Xi Jinping ya yi ga jagororin jam’iyyar, za mu fahimci cewa duk da shekarun da aka kwashe, burin jam’iyyar bai sauya ba, inda take kokarin ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan gina kanta da tabbatar da da’a da fahimta tsakanin al’umma da kuma jagorantar al’ummar Sinawa wajen farfado da kasarsu tare da zamanantar da ita.
Lokaci bai kura wa sauran kasashe na koyi da Sin ba. Sun gwada aron tsare-tsaren kasashen yamma, kuma babu inda hakan ya kai su. Don haka za su iya tsara irin dabarun da ya dace da yanayinsu domin kyautata makomar kasashensu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp