Hukumar Kididdiga Ta Kasa (NBS), ta ce farashin kayayyaki sun kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da a ga hakan tun a shekarar 1996.
Nijeriya dai na fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da sauran nau’ikan kayayyakin amfanin yau da kullum.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Barawo Ne, Sun Kwato Dabbobi 90 A Kaduna
- Abba Gida-Gida Da Gwamnoni 12 Na Fuskantar Rashin Tabbas A Hukuncin Kotun Ƙoli
A rahoton da ta fitar NBS, ta ce an samu karin hauhawar farashin kayayyaki a watan Nuwamba da kashi 0.87 cikin 100, idan aka kwatanta da watan Oktoban da ya gabata.
Hauhawar farashin kaya a Nijeriya yanzu ya haura kashi 27.33 cikin 100 zuwa kashi 28.20 ciki 100, kuma rabon da a shiga irin wannan yanayi na tashin farashin kayayyaki tun 1996.
Kazalika, hukumar ta ce wannan mataki na hauhawar farashin kaya ya karu da kashi 6.73 cikin 100, idan aka kwatanta da watan Nuwamban shekarar 2022, wanda ya ke a matakin kashi 21.47 cikin 100.
Rahoton, ya ce hauhawar farashin kayayyaki na watan Nuwamba ya wuce adadin da aka kiyasta a watan Oktoban da ya wuce.
Rahoton ya ce hauhawar farashin kayan abinci ya karu da kaso 32.84 cikin 100 a shekarar 2023, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata wanda yake a matakin kaso 24.13 cikin 100.
Rahoton, ya kara da cewa kayayyakin da suka ta’azzara hauhawar farashin sun hada da farashin Burodi, man girki, doya da kuma dankalin turawa, sauran kayan kuwa su ne kifi, nama da saura kayan kwalam da makulashe da kuma na shayi.
‘Yan Nijeriya dai na zuba idon ganin abin da gwamnati za ta fito da shi domin kawo karshen yadda farashi kayayyaki ya ke tashi.