Annabi (SAW) yana da Alkebba guda uku, Sundusu Koriya, Jubba mai kokuwa sai Abaya mara kokuwa, akwai rawani na Annabi (SAW) guda biyu, akwai Sahabu (Girgije) da kuma Aswad (Baki wanda aka yi Fat’hu Makkata da shi). Annabi (SAW) yana da Tutar Kasa (Mai Launin Fari) da Tutar yaki mai suna Gaggafa, mai launin Baki.
Annabi (SAW) yana da Mayafi wanda ake ratayawa bayan an sa kaya.
Bayan mun anbaci abubuwa da kayayyakin yakinsa, yanzu za mu ambaci abubuwan hawansa na daga dabbobinsa/dawakansa.
Dawakai a zamanin Annabi (SAW) su ne abin hawa kuma su ne abin hawa a yi yaki, sabida haka, in ana raba kaso na sojojin yaki, soja mai abin hawa ana ba shi kaso biyu sauran kuma a ba su kaso daya.
Doki albarka ce, Annabi (SAW) ya yi addu’a kan doki da cewa, Allah ya bar albarka kan doki har tashin Alkiyama. Doki akwai na Farillah lokacin yaki, akwai na Mustahabbi – doki don Ado da kwalliya, akwai wanda aka kyamata, wanda aka tanada don alfahari. Don haka, wanda ya tanadi Doki, Allah zai rubuta masa lada a kan kashinsa, abincinsa da duk wani motsin dokin har zuwa lokacin tashin alkiyama, sabida haka, wasu suke tanadar doki, ko ba su hau ba suna da lada.
Doki yana da Addu’a karbabbiya da yake yi wa mamallakinshi da yamma inda yake cewa, “Allah ka taimake shi, ka budada masa.”
Annabi (SAW) yana da Dawakai guda 20, su ne kamar haka:
- Sakabu: Yana daga cikin dawakan da Annabi yake sawa a yi tsere da shi, Annabi (SAW) ya kasance yana sa tsere a tsakanin dawakan Sahabbansa zuwa wuri mafi tsawo ko mafi gajarta.
- Murtajibu: ya samo sunansa ne sabida dadin haniniyarsa,
- Garbu: Ana ce masa Garbu ne sabida karfin jikinsa.
- Lahiku: Ya samo sunansa ne sabida kibarsa. Cin doki Halal ne a wasu Mazahaba kamar Shafi’awa amma Malikiyya ba su ci.
- Allizazu: Yana da kyakkyawar halitta, ta cika, Annabi (SAW) ya ambace shi da suna Allizazu.
- Alwardu: Baki ne
- Assaba’atu: Ya samo sunansa ne, a yanayin tsarin gudunsa wanda ya kasance yana mike kafafunsa sosai in yana gudu.
- Albahru: Mai linkaya a ruwa, Annabi (SAW) ya sa masa sunan ne sabida linkayarsa a ruwa.
- Mirwahu: Ya samo sunansa ne sabida yawan tsalle da tashi
- Sijlu
- Zul himmati
- Zul wukari
- Sirhalu
- Durfa
- Almurtajilu
- Milawiku
- Mandubu
- Annajiru
- Alya’azubu
- Alya’asubu
Wadannan su ne dawakan Annabi (SAW) guda 20 da duk al’ummar Annabi (SAW) ta tafi a kansu.
Annabi (SAW) yana da Alfadarai guda biyar (5). Alfadari ana fitar da shi tsakanin Doki da Jaki.
Ga su kamar haka:
- Jundilu: wannan shi ne wanda yafi shahara.
- Hibbatu
- Ailatu: Sarkin Ailatu ne ya bayar da ita ga Annabi (SAW)
- Najjashiyyatu: Sarkin Habasha, Najjashi ne ya bayar da ita ga Annabi (SAW).
- Jandaliyyatu: Sarkin Daumatu Jandal ne ya bayar da ita ga Annabi (SAW).
Annabi (SAW) yana da Jakuna guda Uku (3). Akwai Usaibu, Ya’afur sai wanda Sa’adu bin Ubadata ya ba shi. Sa’adu bin Ubadata yana daga cikin Ansaru kuma shugaba ne, mai arziki ne da ya taso cikin dukiya, ya taimaki Annabi da Sahabbansa sosai, ya yi mubaya’a ga Annabi (SAW) tun ta farko wacce mutanen Madina suka yi da Annabi (SAW) (Murakaba), Sadauki ne, ya yi yake-yake da Annabi (SAW) da yawa amma kaddarar Siyasa ta same shi, Kafin zuwan Annabi (SAW) Madina, shi za a bai wa sarauta bayan zuwan Annabi (SAW), aka bar maganar Sarauta. Yayin da Sayyadina Abubakar ya zama Kalifa bayan rasuwar Annabi (SAW) sai ya ki yin mubaya’a ya tafi Sham ya rasu a kasar. Rasuwarsa ta jawo cece-ku-ce, wasu suka ce, Aljannu ne, wasu suka ce mutuwa ce irin ta kisa a Siyasance (kashe shi aka yi), wasu kuma suka ce, mutuwa ce ta al’ada.
Rakuman Annabi (SAW): Mafi yawanci, Larabawa sun fi hawa rakuma mace, Sabida ba ta da kuka na tonon asiri. Daga cikin rakuman da Annabi (SAW) ke hawa, akwai Kaswa’u (wacce Annabi (SAW) ya yi Hijira zuwa Madina a kanta), Hadba’u, Jad’a’u, Rakumin Abu Jahli wanda ya fada cikin ganimar Annabi (SAW) a yakin Badr da aka gwabza – Annabi (SAW) ya yi Hadaya da shi a Hudaibiyya.
Annabi (SAW) yana da Rakuma Mata 45 wadanda ya raba wa Matansa, Sa’adu bin Ubadata ne ya bai wa Annabi (SAW) rakuman. Ummu Salamata ta ce, “Nagode Allah, wacce aka ba ni, tana bayar da nono fiye da na rakuma biyar.” Daga cikin Rakuman 45, Malamai sun rahoto sunayen guda 25, yanzu gaba daya, an ambaci guda Uku da suna kamar yadda muka kawo a sama, in an hada da sunayen guda 25, zai zama, akwai Rakuma guda 28 na Annabi da aka ruwaito sunayensu.
Sunayen Rakuma 25 daga cikin 45 da Sa’adu bin Ubadata ya bai wa Annab (SAW) ga su kamar haka:
Adlalu, Adrafu, Burudatu, Barakatu, Bagumu, Hanna’u, Balzamu, Arraya’u, Sa’adiyyatu, Assukya, Assamra’u, Ashshakra’u, Adrasu, Kuraishun, Gaisatu, Kamaru, Marwatu, Mihratu, Wirshatu, Yukairatu.
Sa’adu bin Ubadata, mutumin Madina ne, Alkazraji, ya yi Bai’atul Ukbatu, mai kyauta ne, ya taimaki Sahabbai da yawa, in Sahabbai suka ga mai jin yunwa, sai su kai shi gidan Sa’adu a ciyar da shi, ko yana nan ko baya nan za a ciyar da shi abinci, har bayan rasuwar Annabi (SAW), duk matan Annabi (SAW), kowacce akwai kwanon Abincinta a gidan Sa’adu, Sadauki ne mai rike da Tuta. Bayan rasuwar wadanda ke rike da tutar Muhajirai, sai Annabi (SAW) ya mika ta ga Sayyadina Ali, Sa’adu kuma yana rike da tutar Ansaru. Sa’adu yana rike da tutar Ansaru har sai lokacin Fat’hu Makkah yayin da ya ce, “Yau ce ranar kai dauki ga Makkah,” sai Annabi (SAW) ya ji tsoron kar a halatta jini a Makkah, sai aka amsa tutar aka bai wa dansa. Sa’adu ya kware sosai a wurin harbi, ya rasu a garin Haurana da ke kasar Sham, an same shi matacce a cikin bandakin wankansa, jikinsa ya yi kalar Kore.
Sa’adu bin Ubadata, bayan rasuwar Annabi (SAW), shi ne wanda mutanen Madina suka hadu suka ce shi ne Kalifansu, yayin da Sayyadina Abubakar ya samu labarin hakan, sai ya dauki Sayyadina Umar zuwa wurin inda Mutanen Madina suka taru, da isarsu wurin, Sayyadina Umar ya fara yi wa Sayyadina Abubakar Mubaya’a sannan sauran Sahabbai don guje wa fitina, amma Sa’adu bai yi hikima irin ta Sayyadina Ali ba, sai ya bijire ya ki bin Sayyadina Abubakar, ya bar Madina zuwa Sham inda ya rasu.
Mutane Uku ne suka yi takarar kalifanci: Sayyadina Abubakar – Sayyadina Umar ne ya nada shi sai Muhajirai suka goyi baya; Sayyadina Ali – shi kuma da ya ga muhajirai sun goyi bayan Sayyadina Abubakar sai ya yi shiru; na Ukunsu shi ne, Sa’adu bin Ubadata – shi kuma ya ce, ba zai bi Sayyadina Abubakar cikin komai ba.
Rasuwar Sa’adu tana dabaibaye da rudani sakamakon ganin gawarsa a cikin bandaki. Wasu sun ce, an ji Aljanu suna wake da cewa, su suka harbe shi, kuma alamu sun nuna hakan yayin da aka ga jikinshi ya yi kalar Kore; a wani zance kuma, kamar masu ra’ayin shi’a, suna cewa, wannan shi ne kisa na farko da aka fara yi sabida siyasa wasu kuma sun tafi cewa, mutuwa ce irin ta al’ada ta riske shi.
A kowane hali dai, Sa’adu ya taimaki Annabi (SAW) da abubuwa masu yawa da Annabi (SAW) ya rayu a kansu, Allah ya karba masa Shahadarsa.
Yana daga cikin Addu’ar da Annabi (SAW) ya yi masa da cewa, “Ya Allah ka sanya Sallolinka da albarkokinka duka a bisa iyalin gidan Sa’adu bin Ubadata.”
Annabi (SAW) yana da tumakai guda 100 da ake yi masa kiwo, Annabi (SAW) bai tara duk wannan dukiya ba don kansa sai don ciyar da Ahlus-sifati kusan 700 da suke zaune a gidansa, ba su zuwa ko ina sai zikiri da haddar addini (ilimi) a Masallaci.