Yayin da bikin bazara na shekarar Loong wato Dragon a Turance na kasar Sin ke karatowa, yanayin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar na karuwa. A halin yanzu, kusan kasashe 20 na duniya sun ayyana bikin bazara a matsayin lokacin hutu a hukumance, kuma kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya ne ke murnar bikin bazara ta hanyoyi daban-daban.
Kwanan nan, wani faifan bidiyo game da ‘yan kasashen waje dake sayen kayayyakin sabuwar shekara na yaduwa a yanar gizo, wato wata ‘yar Burtaniya ta tallata motoci kirar kasar Sin masu amfani da wutar lantarki a matsayin kyautar sabuwar shekara, inda ta ce za ta ba dan uwanta daya.
Ana sha’awar sayen kayayyaki kirar kasar Sin a kasashen ketare ne ba a lokacin bikin bazara kadai ba. Ya zuwa yanzu, kayayyaki kirar kasar Sin na kara samun karbuwa a ketare. Mene ne dalilin? “Kayayyaki masu inganci” su ne abu na farko da masu sayayya ke bukata. Fifikon da kasar Sin ta samu wajen tsarin masana’antu da na samar da kayayyaki a cikin dogon lokaci, shi ma yana taimakawa kayayyaki kirar kasar wajen samun karbuwa a duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)