A cikin rubu’in farko na bana, harkokin yawon shakatawa a Sin sun farfado sosai, inda yawan kayayyakin shige da fice ya kai yuan biliyan 337.63, wanda ya karu da kashi 56.6 cikin dari bisa makamancin lokaci a bara.
Daga cikinsu, fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ya karu da kashi 38.4 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara, sannan shigo da kayayyaki ya karu da kashi 58 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara.
Bisa kiddidigar da ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta bayar a ranar 9 ga wata, a rubu’i na farko, cinikin ba da hidima ya ci gaba da karuwa. Kuma jigilar kayayyakin da aka shigo da fitar da su ya kai yuan triliyan 1.58401, wanda ya karu da kashi 8.7 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara. Haka zalika cinikin ba da hidima mai alaka da ilmi ya karu sosai, wanda ya zama wani sabon salo. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp