Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya tabbatar da cewa ya dawo da wutar lantarki a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), bayan raɗe-raɗin cewa asibitin ya rasa wuta har yayi sanadiyar asarar rayuka.
Jami’in hulɗa da jama’a na KEDCO, Sani Bala Sani, ya bayyana cewa matsalar ta taso ne sakamakon shirin da ake yi na raba layin wutar da ke bai wa asibitin da kuma gidajen ma’aikata. Ya ce an haɗa asibitin ne kai tsaye da “33kV Zaria Road feeder” wanda ke samar da kimanin wutar awanni 22 na wuta kullum a ƙarƙashin Band A.
- Firaministan Nepal: Sin Ta Samu Cikakken Ci Gaba Daga Dukkanin Fannoni
- Katsewar Wutar Lantarki: Mun Yi Asarar Fiye Da Naira Biliyan 6 – KEDCO
Sai dai ya ce Asibitin AKTH ya dage kan cewa gidajen ma’aikatansa su ci gaba da amfani da layi ɗaya da asibitin, abin da ya janyo matsaloli masu tsanani har ya haifar da katsewar da aka samu. Don kaucewa sake faruwar hakan, KEDCO ta yi raba layukan domin tabbatar da samun ingantacciyar wuta ga asibitin.
KEDCO ta kuma bayyana cewa tana bin asibitin bashin kuɗin wutar lantarki sama da miliyan ₦949 na tsawon lokaci, inda aka buƙaci ya biya cikakken kuɗin watan Agusta 2025 na ₦108.9m cikin kwanaki goma don gujewa ɗaukar matakai kan wasu wuraren da ba na sashin gaggawa ba na Asibitin.
Kamfanin ya jaddada cewa zai ci gaba da bai wa asibitoci fifiko wajen samar da wuta, musamman sashin dake bayar da aiyukan ceto rayuka, tare da roƙon shugabancin AKTH da ya haɗa kai da tsarin raba layin don amfanin marasa lafiya da al’umma baki ɗaya.