Wani abin takaici ya afku a karamar hukumar Agatu da ke jihar Benuwe a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin da wani kwale-kwalen da ke dauke da iyali mutum bakwai ya kife a Obagaji, inda ‘yan’uwa biyar suka rasu.
A yayin tattaunawa ta wayar tarho da wani mai suna John ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da wani karamin kwale-kwale dauke da wani mutumi da matarsa da ‘ya’yansa biyar ya kife da su a cikin kogin.
A cewarsa, an ceto mutumin da matarsa da ransu amma duk yaran biyar sun nutse kafin a kai musu dauki.
Wani da ya sake shaida lamarin, Ameh Ejeh, ya ce da faruwar lamarin, masu iyo suka kaddamar da aikin ceto, sai dai duk yaran biyar an tabbatar da mutuwarsu bayan zakulo su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp