Farin jinin fadar White House da majalisar dokokin kasar Amurka, na ci gaba da raguwa, a cewar wani sabon bincike na Gallup.
A cewar rahoton, kaso 40 cikin 100 ne mutanen da aka tambaya, sun nuna amincewa da kimar shugaban Amurka Joe Biden, inda kashi 55 cikin 100 suka nuna rashin amincewa da yadda yake tafiyar da aikinsa.
Kuri’ar nuna rashin amincewa da Biden, ta ci gaba da karuwa, tun watan Satumban shekarar 2021, bayan ficewar sojojin Amurka daga kasar Afghanistan.
A halin da ake ciki, yadda Amurkawa ke nuna rashin amincewa da majalisar dokokin kasar, ba shi da kyau ko kadan, inda kashi 73 cikin 100 na baligai Amurkawa ke nuna rashin amincewa.
An wallafa sakamakon wannan binciken kuri’ar jin ra’ayin jama’a ne daga ranar 9 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamba, wanda Gallup ya gudanar bayan zaben tsakiyar wa’adi na ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar 2022.
Sharhin da Gallup ya rubuta, ya bayyana cewa, majalisar dokokin Amurka za ta fuskanci rabuwar kai a cikin shekaru biyu masu zuwa, bayan da ‘yan jam’iyyar Republican suka kwace ikon majalisar, yayin da ‘yan Democrat ke da rinjaye a majalisar dattawa. (Ibrahim Yaya)