• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kimiyya Na Inganta Zaman Rayuwar Sinawa

by CMG Hausa
3 years ago
Kimiyya

A kwanakin baya, na raka abokiyar aikina Fa’iza Mustapha, wajen daukar wani bidiyo, inda ta gwada fita unguwa ba tare da daukar jakar kudi ba.

A cikin bidiyon, ta je wurin shan kofi, da motsa jiki a cikin Gym, da sayen kayayyakin abinci a kasuwa, da shiga jirgin dake gudu a karkashin kasa, da hawan keke na haya, inda a duk wadannan wuraren ta biya kudi ne ta wayar salula.

  • Masani: Amurka Take Yada Karairayin Aikin Tilas Don Bata Sunan Kasar Sin

Ta gaya mana cewa, da wayar salula, ana iya gudanar da harkokin yau da kullum a kasar Sin, hakan yana da sauki, gami da tsaro.

Hakika a nan kasar Sin, ban da yin amfani da wayar salula wajen biyan kudi, ana iya sayen kayayyaki a shafukan Internet, da sanyen tikiti na jirgi, da tikitin kallon nune-nune, da yin rajista kafin a je asibiti, ko kuma kafin a ziyarci wani wurin adana kayayyakin tarihi, da dai sauransu. Sai dai duk wadannan abubuwa wani bangare ne na amfanin kimiya da fasaha a zaman rayuwar al’ummar Sin.

Kimiyya
dav

A nan kasar Sin, mutane sun saba da gudanar da taro ta kafar Internet, da tara bayanai da wata manhaja ta musamman yayin da ake aiki. Sa’an nan bayan sun koma gida, suna amfani da wata na’ura wajen yi wa kansu tausa, da dandana abincin da aka yi girkinsu ta wasu na’urori masu sarrafa kansu, yayin da wani Robot ke kokarin tsabtace dakuna.

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Dalilin da ya sa Sinawa ke iya more zaman rayuwa mai kunshe da fasahohin zamani shi ne, gwamnatin kasar ta dora muhimmanci sosai kan raya kimiya da fasaha.

A ganinta, sabbin fasahohi suna iya samar da sabbin bukatu a kasuwa, da sabbin guraben aikin yi, ta yadda za su sa kaimi ga karuwar tattalin arziki, da ci gaban kasa.

Saboda haka, cikin shekaru 10 da suka wuce, kudin da kasar Sin ta ware don raya kimiya da fasaha ya karu, daga dalar Amurka biliyan 153.9 zuwa biliyan 416.8. Kana daga shekarar 2012 zuwa ta 2021, jimillar tattalin arzikin kasar a fannin fasahohin zamani ta karu, daga dalar Amurka biliyan 1643.4 zuwa fiye da biliyan 6723, yayin da adadin wannan bangare a cikin GDPn kasar ya karu daga kashi 21.6% zuwa 39.8%.

Ban da haka, yadda Sinawa suke maraba da sabbin fasahohi, shi ma ya taimakawa raya wannan bangare a kasar. Misali, bayan an samu fasahar sadarwa ta 5G, mutane suna son gwada ta, maimakon su amince da jita-jitar da aka yada, wai fasahar tana iya lahanta lafiyar jikin dan Adam.

Kana bayan da aka fara ganin motocin Taxi marasa matuka a kan titi, mutane suna son gwada zirga-zirga da su, maimakon tsoron yiwuwar “inji ya kwace aikin mutum”. Saboda tuni aka samu shaidu daga tarihin dan Adam, cewa sabbin fasahohi za su inganta masana’antu, tare da samar da sabbin guraben aikin yi, da ingantaccen muhallin aiki, maimakon kwace guraben aiki kawai.

Yadda kasar Sin take son hadin gwiwa da sauran kasashe, ya sa ci gabanta a fannin kimiya da fasaha ke samar da alfanu ga mutanen duniya.

Yanzu haka wayoyin salula kirar kasar Sin, wadanda suke kayatar da hotunan da aka dauka na samun karbuwa tsakanin samari, da ‘yan mata na Najeriya, kana sauran fasahohin kasar Sin irinsu biyan kudi ta wayar salula, da ta keken haya na zamani, dukkansu sun shiga kasuwannin Afirka.

Nan gaba, za mu iya ganin yadda karin fasahohin kasar Sin ke ba da taimako wajen kyautata zaman rayuwar jama’ar kasashen Afirka, kamar yadda suke haifar da ci gaban al’umma a nan kasar Sin. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
Next Post
NDLEA Ta Bankado Hodar Iblis Da Aka Boye Cikin Abincin Jarirai

NDLEA Ta Bankado Hodar Iblis Da Aka Boye Cikin Abincin Jarirai

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.