Ranar 20 ga watan da muke ciki, kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri’a kan daftarin kudurin tsagaita bude wuta a Gaza da mambobi 10 na kwamitin wadanda ba na dindindin ba suka gabatar. Kudurin ya samu kuri’u 14 na nuna amincewa, da kin yarda 1 daga Amurka.
Wannan ya kasance karo na 5 da Amurka take kin yarda da daftarin kudirin tsagaita bude wuta a Gaza tun barkewar rikicin zirin Gaza na wannan karon. Lokacin da Amurka ta nuna kin yarda da shi a karon farko a ranar 18 ga watan Oktoban na bara, jama’a fiye da 3000 sun rasa rayukansu a yankin, a halin yanzu wannan adadi ya karu zuwa 44000, amma Amurka ta ci gaba da hawan kujerar na ki a bangarenta.
- Kamata Ya Yi Sin Da Amurka Su Mai Da Hankalinsu A Kan Ci Gaban Duniya
- Za Mu Kawo Karshen Hukunce-Hukuncen Kotuna Masu Karo Da Juna – Minista
Rayukan mutum 44000 ba adadi ne kawai ba, ainihin rayuka ne. Jama’ar Gaza na mutuwa a cikin hare-haren da ake kai musu. Kasashen duniya na yin iyakacin kokarin fitar da hanyar da ta dace wajen warware wannan matsala, don hana tsananta halin da ake ciki a yankin. Amma, Amurka ta yi amfani da ikonta na kin amincewa sau da dama, har ma ta samarwa Isra’ila da tallafin makamai sau da dama, matakin da ya rika tsananta halin da ake ciki. A gaskiya abin kunya ne ga gwamnatin Amurka, wadda ta rasa jin tausayi ko nuna halin mutunci da adalci.
Matakan soja da Isra’ila ta dauka a Gaza sun wuce matakin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma gindaya sharadi wajen tsagaita bude wuta, tamkar rura wutar yaki ne da kisan jama’a. Daina bude wuta ba tare da sharadi ba nan da nan da tabbatar da shirin “samar da kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo da za a warware wannan matsala. Don haka, bai kamata Amurka ta yi amfani da ikonta na hawan kujerar na ki a kwamitin sulhu ba don kare moriyarta da ba da kariya ga kawayenta. Amurka, dole ne ta nuna mutunci da kuma adalcinta a fili a kan wannan lamarin. (Mai zane da rubutu: MINA)