Dattijo kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ambasada Babagana Kingibe, ya yaba wa Ambasada Tukur Yusufu Buratai bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban ilimi a Nijeriya, musamman a fannin bunkasa jagoranci matasa da tunani mai zurfi.
Ambasada Kingibe, wanda ya yi wannan yabo a lokacin da yake jagorantar bikin bayar da lambar yabo ta 2024 na Adabin Matasa da kungiyar TY Buratai Literary Initiatibe (TYBLI) ta shirya, ya yaba da kwazon Buratai a kakarinsa na renon matasa.
- Kamfanoni 80 Sun Bayyana Burinsu Na Halartar Baje Kolin CIIE Karo Na 8
- Zargin Cin Zarafin Likita: Gwamna Yusuf Ya Roki Likitoci Su Bayar Da Kofar Sulhu
Da yake tunawa da shekarun da ya yi a aikin soja, Ambasada Kingibe ya tunatar da gagarumin sauyi da sojoji suka samu a lokacin jagorancinsa a matsayin shugaban soji da kuma kwazo da ci gaban tunani na hafsoshi da sojoji.
Ambasada Kingibe ya jaddada karfin adabi mai dorewa a matsayin ginshikin sadarwa mai inganci, duk da ci gaban ada aka samu ta fuskar ilimn fasahar zamani.
“Fasaha ba zai iya sauya salon rubutacciyar kalmar ba,” in ji shi, ya yi alkawarin hadin gwiwa a cikin shiri na gaba na TYBLI don ci gaba da horar da matasa masu basira a Nijeriya.
A nasa jawabin, babban mai masaukin baki kuma tsohon Hafsan Sojin Kasa, sannan tsohon jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai mai ritaya, ya jaddada mahimmancin rubutu wajen ci gaban mutum, sadarwa, da jagoranci.
“Rubutu na da matukar muhimmanci wajen bunkasa ilimin mutum, hangen nesa, da kuma ikon sadarwa,” in ji shi. “Dole ne shugabanni su bayyana ra’ayoyinsu, kuma don ku bayyana kanku da kyau, dole ne ku rubuta.”
Da yake waiwaye kan kwarewarsa a matsayinsa na dan kungiyoyin adabi da wasan kwaikwayo a shekarunsa na makaranta, Buratai ya jaddada mahimmancin rubutu don ci gaban kansa, sadarwa, da jagoranci. “Dole ne shugabanni su bayyana ra’ayoyinsu.
Idan ba ku rubuta abin da kuke tunani ba, kuna iya mantawa da shi.
Amma da zarar ka rubuta shi, yana bude damar da za a amfana da al’umma.” A cewarsa.
Ya nuna godiya ga mahalarta taron, magoya baya, da abokan hadin gwiwa, ciki har da Hajiya Hauwa Aliyu da British Council.
Buratai ya kuma yi tsokaci kan shirin kara kudaden kyaututtuka da kuma yiwuwar bayar da tallafin karatu ga wadanda suka yi nasara a karatun sakandare ko na gaba.