Bana shekara ce ta cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. A cikin shekaru 75 da suka gabata, bangaren kimiyya da fasaha ba ma kawai ya ingiza zamanantarwar kasar Sin ba, har ma ya sa kaimi ga bunkasuwar kimiyya da fasaha a duniya, da masana’antu masu fasahohin zamani, tare da ba da gudummawa ta hakika ga ci gaban dan Adam. Kana alkaluman karfin kirkire-kirkire na duniya na shekarar 2024 da hukumar ikon mallakar fasaha ta duniya ta fitar sun nuna cewa, karfin kasar Sin a fannin kirkirar sabbin fasahohi ya tashi da matsayi daya zuwa na 11, daga matsayi na 12 a bara.
Musamman ma a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, kasar Sin a ko da yaushe ta nace kan inganta bangaren kimiyya da fasaha da dogaro da kai, tare da yin amfani da damar samun ci gaba da sabon zagaye na juyin juya halin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen salon masana’antu suka haifar, da samun sabbin fasahohi a kai a kai. Daga cikin su, masana’antar sarrafa sabbin makamashi ta zama tamkar wani sabon katin kasuwanci na kasar Sin, wadda ba ma kawai ta samar da dimbin kayayyaki ga kasuwannin kasa da kasa, da sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma ta hanyar kare muhalli ba, har ma ta ba da gudummawa sosai ga ayyukan tinkarar sauyin yanayi a duniya, da sauye-sauyen salon makamashi zuwa wani mai kare muhalli.
Fasaha ba ta san iyakokin kasa ba. A mahangar kasar Sin, ba za a iya raba sabbin fasahohi da hadin gwiwar da kasar take yi da sauran kasashe ba, wanda wani muhimmin ilimi ne da kasar Sin ta samu, yayin da take neman ci gaban bangaren kimiyya da fasaha. Ta hanyar yin hadin gwiwa da karin kasashen waje a fannin kimiyya da fasaha, kasar Sin ta sa kaimi ga raba dimbin sakamakon da aka samu a fannin kimiyya da fasaha, ta yadda duk duniya za ta samu ci gaba na bai daya a wannan fanni. (Bello Wang)