Wasu da ba a san ko su waye ba, sun kone wasu sassan kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta inda aka kashe sojoji 16.
Sai dai, an yi ta rade-radin cewa, watakila wasu sojojin da suka fusata ne suka aikata hakan biyo bayan kashe abokan aikinsu.
- Kane Ya Samu Rauni A Kafarsa Ana Gab Da Buga Wasa Tsakanin Ingila Da Brazil
- An Kusa Raba Gari Tsakanin Mbappe Da PSG
A yanzu haka dai, ana ci gaba da farautar wadanda suka kashe jami’an ssojn yayin da aka kama wasu da ake zargi a kauyen karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta 6 ta sojojin Nijeriya, Manjo Janar Jamal Abdussalam.
An ce mazauna yankin sun tsere zuwa garuruwan da ke makwabtaka da kauyen Ughelli saboda fargabar ramuwar gayya daga sojojin da ke sintiri a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp