Kishin kasa a koda yaushe babban jigo ne mai karfafa gwiwa, da karfafawa ga jama’a daga dukkan kabilun kasar Sin, da ba su kwarin gwiwar neman ci gaba da inganta kansu.
Na saurari kuma na karanta a jaridu da mujallu bayanan Shugaba Xi Jinping inda yake yawaita karin haske kan kishin kasa a lokuta da dama. Yana mai jaddada cewa, “dole ne mu sa kaimi ga kishin kasa, a kokarin da ake yi na cimma babban farfadowar al’ummar kasar Sin.” Kishin kasa da shugaba Xi yake da shi, shi ne ke ingiza kishin kasa dake cikin zukutan Sinawa wanda ya zama mabudi da wadatar kasar Sin.
Yadda sinawa ke kishin kasarsu ya bayyana a irin biyayyar da suke ma shugabanni da gwamnatin kasar, da tabbatar da tsare-tsare da ka’idojin gudanar da ayyukan yau da kullun da bin doka da oda.
A tsawon tarihin kasar Sin da ya shafe dubu-dubatar shekaru, kishin kasa ya kasance wani karfi na ruhaniya wanda ya hada al’ummar kasar Sin tare da karfafa gwiwar al’umman Sinawa da za su biyo baya da su ci gaba da himmatuwa don bunkasuwa da wadatar kasarsu ta haihuwa.
Kasar Sin ta ciri tuta a duk wani fannin da ya shafi ci gaban rayuwa musamman na zamani a dalilin himmatuwar ’yan kasa wadanda a kullum burinsu shi ne ci gaban kasar Sin, wannan shi ne sakamakon kishin kasarsu dake tattare da su.
Masu iya magana kan ce “Komai tsayin inuwar bishiya, saiwarta na ci gaba da yin girma a ƙasa”. (Yahaya Babs)