A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa a dangantakar Sin da Amurka, ya dace da moriyar jama’ar kasashen biyu, da kuma fatan al’ummomin duniya baki daya.
Dangane da rikicin Ukraine kuwa, Guo Jiakun ya ce a baya-bayan nan, kungiyar “Kawancen zaman lafiya” kan rikicin Ukraine ta gudanar da wani taro a birnin New York, domin tattauna halin da ake ciki game da rikicin Ukraine, da kuma fatan samun dauwamammen zaman lafiya.
Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, wajen taka rawa mai ma’ana, don cimma nasarar warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp