An haifi shahararren jarumin nan na Masana’antar Bollywood, Amrish Puri da aka fi sani da Mogembo; ranar 22 ga watan Yunin shekarar 1932, a Kauyen Nawanshahr na jihar Punjab da ke Kasar Indiya.
A koda-yaushe, za a ci gaba da tunawa da Mogambo a matsayin wanda ya taka muhimmiyar rawa a tarihin fina-finan Kasar Indiya, musamman bangaren fitowa a matsayin Uban Daba.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 16 A Kaduna
- ‘Yan Bindiga Ne Suka Kawo Cikas Ga Samar Da Isasshiyar Wutar Lantarki Ga ‘Yan Nijeriya A 2024 – Minista
Amrish, ba haka kawai ya samu kansa a matsayin jarumin fim ba, domin kuwa ya tashi ya iske a gidansu ana yin wannan sana’a ta fim.
Kazalika, ya shafe fiye da shekaru 20 ana damawa da shi a Masana’antar Bollywood, duk da ya samu daukaka matuka; amma bai shiga wannan harka ta fim ka’in da na’in ba, sai da ya fara koyon sana’ar daga tushe; domin kuwa ya yi aiki a makarantar koyon dirama da ke Delhi, kafin ya shiga wannan masana’anta.
Haka nan, Mogambo ya yi ayyuka da dama a wurare daban-daban; amma bayan shigarsa harkar fim din ne ne aka gano yana da wata baiwa ta musamman, wanda hakan ya ba shi damar samun daukaka a masana’antar.
A shekarar 1971, ya fara fitowa a matsayin jarumi a Bollywood tare da Reshma Aur Shera; amma an fi sanin sa a shekarar 1980, lokacin da ya fara fina-finai a matsayin Uban Daba ko babban bos.
Fim din da ya fito a shekarar 1987 na Mista Indiya da ya fito a matsayin Magambo, ya sa duniya ta san shi; ya kuma samu masoya da dama tare da kasancewa guda cikin fitattun jarumai Iyayen yen Daba da aka taba samu a tarihin masana’antar ta Bollywood.
Har ila yau, ya ci gaba da fitowa a wannan matsayi a fina-finai daban-daban da suka hada da Bidyapati(1986) da kuma Darr(1993), wanda ya sa a wancan lokacin ya zama jarumi ko babban bos mafi shahara da daukaka a fina-finan Kasar Indiya.
Bayan fitowa a matsayin babban bos, Amrish ya kan fito a matsayin mataimakin jarumi ko uba a wadansu lokutan; wanda kuma hakan ya sake nuna bajintarsa a dukkanin inda ya samu kansa a cikin shirin fim.
Bugu da kari, ya shiga idon duniya ne a lokacin da ya fito a wasu fina-finai na Kasar Amurka da suka hada da ‘Indiana Jones da kuma Temple of Doom’ a shekarar 1984, inda ya taka rawar wani mai suna Mola Ram, wanda hakan ba karamin ci gaba ya jawo wa rayuwarsa a matsayinsa na jaumi ba.
Mogambo, ya rasu ranar 12 ga watan Janairun shekara ta 2005; amma har yau ba a samu wani wanda ya maye gurbin da ya bari a Bollywood ba, sannan kuma ya zama abin koyi a wajen jaruman Bollywood na wa
nnan zamani.