Mai taimaka wa shugaban ƙasa a kan kafafen yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa ko baya cikin gwamnatin Bola Tinubu, ba zai shiga zanga-zangar da ake kokarin yi a watan Agusta ba.
Abdulaziz, ya bayyana haka ne a shafinsa Facebook a safiyar yau Laraba, inda ya mayarwa da waɗanda suke nemo tsofaffin rubuce-rubucensa na baya da ya yi na shiga zanga-zanga.
- Babu Tabbacin Ko Ederson Zai Ci Gaba Da Zama A Manchester City – Guadiola
- Sojoji Sun Sake Ceto Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok
Ya ce “Masu tone-tonen tsoffin rubutuna ba sai kun ba wa kanku wahala ba!
“Na shiga zanga-zanga guda biyu a baya. Na shiga ta cire tallafin man fetur a 2012 a Kano na kuma shiga ta ‘Bring Back Our Girls’ a Abuja a 2014. Duka wadancan zanga-zanga suna da tsari da shugabanci da kuma sanin inda aka dosa.
Yawanci kafin fita zanga-zanga ana fitar da tsarin yadda za ta gudana da kuma irin abin da masu zanga-zangar suke buƙata, hakan ya sa Abdulaziz ya ce wannan ba ta da tsarin da ya kamata a shiga.
“Amma a 2019 ban shiga zanga-zangar ENDSARS ba saboda (kamar yadda na faɗa a wancan lokacin) ba ta da tsarin shugabanci da takamammiyar manufa (idan ban da ƙoƙarin tunzura mutane da yi wa gwamnati tawaye wadda kuma kan kai ga jefa ƙasa cikin ruɗani). Na ɗauki wannan matsayar ne duk da bani da alaƙa ta kusa ko ta nesa da gwamnatin Buhari.
“Zanga-zangar da ake shirin yi ta August b ata da bambanci da ta Endsars don haka ko da ba na cikin gwamnati ba zan taɓa goyon bayanta ba.”
Batun zanga-zanga dai shi ne abin da ake yawan tattaunawa a shafukan sada zumunta a Nijeriya a ‘yan kwanakin nan, sai dai har yanzu ba a san jagororin zanga-zangar ba.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta bakin ministan yaɗa labarai, ya roƙi matasan da suke shirya zanga-zangar da cewa su sake bashi lokaci domin ya saisaita lamuran ƙasar nan.
Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne a jam’iyyar adawa ta PDP, ya soki gwamnatin tarayya, inda ya ce waɗanda suke cewa ka da a yi zanga-zangar su ne waɗanda suka jagoranci wadda aka yi a baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp